Wasu mutum uku sun shiga hannun hukuma kan zargin sun yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyade.
’Yan sanda sun kama mutanen ne bayan sun yi wa yarinyar aika-aikan a yankin Okpella da ke Ƙaramar Hukumar Etsako ta Gabas a Jihar Edo.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Umoru Ozigi na ya sanar da haka a lokacin da matar gwamna jihar, Misis Edesili Anani, ta ziyarce shi a ofishinsa.
Matar gwamnan ta yaba masa kan ɗaukar mataki cikin gaggawa bayan ɓullar bidiyon da masu fyaɗen suka ɗauka a yayin da suke wa yarinyar aika-aikan a ranar jajibirin Kirsimeti.