Jami’an lafiya a kasar Isra’ila sun tabbatar da mutuwar mutane 44 sakamakon wata turereniya yayin wani taron addinin Yahudawa a kasar.
Ma’aikatar Lafiya ta kasar a ranar Juma’a ta ce karin wasu mutane 150 kuma sun sami raunuka kuma yanzu haka suna can kwance a wasu asibitoci guda shida na kasar.
- Batanci ga Sahabbai: An dakatar da malami daga yin wa’azi a Bauchi
- Bashin da ake bin Najeriya ya doshi Naira tiriliyan 34
An dai shirya taron gangamin ne domin bikin ranar Lag B”Omer, wani biki da ake yi a kowacce shekara inda a kan yi kade-kade da raye-raye a tsaunin Meron.
Garin na Meron dai nan ne kabarin daya daga cikin manyan waliyyan Yahudawa, Rabbi Shimon Bar Yochai yake, kuma yana daya daga cikin garuruwa mafiya tsarki ga Yahudawan.
Hukumomi a kasar sun ce mutanen da suka halarci bikin za su kai kusan 10,000, amma kafafen watsa labarai sun tabbatar da cewa adadin zai iya rubanya haka har sau 10.
Rahotanni sun ce turereniyar ta fara ne lokaicn da mutane suka fara zamewa suna faduwa a kan wani karfe mai santsi, lamarin da ya sa mutane da yawa suka rika fadawa suna danne ’yan uwansu.
Sai dai shaidun gani da ido sun zargi ’yan sanda da yin sakaci ta hanyar barin mutane su cunkushe wurin, duk kuwa da sun san cewa ya riga ya cika ba masaka tsinke sannan kuma suka ki bude hanyoyin ficewa cikin gaggawa lokacin da iftila’in ya fara.