✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 40 sun mutu a wajen hakar ma’adinai a Kwango

Kasar ta rufta da su ne ranar Talata

Hukumomi a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango sun tabbatar da mutuwar mutum 40 a wajen hakar ma’adinai bayan kasa ta rufta da su a tsakiyar kasar.

Ministan Harkokin Cikin Gidan kasar, Alain Tshisungu Ntumba, ya ce lamarin ya faru ne a yankin Samba ranar Talata.

Ya ce tuni aka gano gawarwakin mutum shida, yayin da ake ci gaba da aikin ceto don tono ragowar mutanen daga karkashin kasa.

Ya ce dukkan wadanda lamarin ya shafa masu hakan ma’adinai ne a ramukan karkashin kasa.

Ministan ya kuma ce lamarin ya shafi rijiyoyin hakar ma’adinan fiye da 40 masu zurfin mita 15 zuwa 18.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa kasar dai na da tarin ma’adinan karkashin kasa kamar su zinari da azurfa da lu’u-lu’u da dai sauransu.

(NAN)