Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta kama wasu mutum 13 ’yan kasar China da ake zargi da hakar ma’adinai ta haramtacciyar hanya a Jihar Kwara.
Da yake yi wa ’yan jarida bayani a ofishinsa, Kwamandan dakarun EFCC shiyyar Ilorin, Michael Nzekwe, ya ce an kama mutanen ne a ranar Laraba a cikin Gandun Dajin Gwamnati dake birnin Ilorin.
- Matar Tinubu ta ba wadanda ambaliyar TradeMore ta shafa a Abuja N250,000
- Za a kashe wa sababbin ’yan majalisa biliyan 70 a matsayin kudaden ‘maraba’
Ya ce 12 daga cikinsu maza ne, sai mace 1 da ke tare da su.
Nwekwe ya ce an yi nasarar kama su ne bayan samun bayanan sirri a kan aikin da suke yi na ta haramtacciyar hanya kuma ba tare da biyan haraji ga Gwamnatin Tarayya kamar yadda dokar kasa ta tanadar ba.
Kwamandan ya ce a binciken da suka gudanar, sun gano cewa kafin a kama wadannan mutanen, ’yan kasar China sun riga sun mamaye kusan duka Kananan Hukumomi 16 inda suke yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ta hanyar hakar ma’adinai ba tare da izni ba.
A cewarsa, yanzu haka sun fara bin sawu domin gano maboyar wasu ’yan Najeriya da suke gudanar da wannan danyen aiki tare domin gurfanar da su gaban kotu.