Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC), reshen Jihar Bauchi, ta tabbatar da rasuwar mutum hudu, yayin da wasu bakwai suka jikkata sakamakon wani hatsarin mota da ya afku a ranar Lahadi.
Kwamandan hukumar a Jihar, Yusuf Abdullahi, ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawarsa da Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN), ranar Litinin a Bauchi.
- ’Yan bindiga sun aure 13 cikin daliban FGC Yauri da suka sace
- Dalilin da tattalin arzikin Najeriya ya bunkasa —Farfesa Darma
Sanarwar ta ce “Mutum 14 ne hatsarin ya rutsa da su, maza tara da mata hudu, sai karamar yarinya guda daya.
“Hudu daga cikinsu sun rasa rayukansu, sai kuma maza biyar da mata biyu da suka ji mummunan rauni,” a cewarsa.
Ya ce hatsarin ya faru ne tsakanin wata mota kirar Sharon mai lamba TRR 391 YX da wata mota Opel Salon mai lamba AA 268 SHR, a kan hanyar Bauchi zuwa Kano, da misalin karfe 2:45 na yammacin ranar Lahadi.
Yusuf ya kuma ce bincikensu ya gano hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce sa’a da motocin biyu ke yi.
A cewarsa, tuni jami’an hukumar suka kai gawarwakin wanda suka rasu babban asibitin kwararru na Jihar, yayin da wanda suka ji rauni na ci gaba da karbar kulawa daga likitoci.