✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 4 sun gurfana a gaban kotu kan zargin satar waya

Alkalin kotun ya ba da belin kowannensu kan kudi Naira 100,000.

An gurfanar da mutum hudu a gaban wata kotu da ke yankin Gwagwalada a Abuja, bisa zarginsu da satar wayar salula da kudinta ya kai N54,000.

Wadanda ‘yan sandan ke zargi dukkansu mazauna garin Giri ne a babban birnin tarayya, wadanda ake tuhuma da laifuka uku da suka hada da hadin baki, cin zarafi da kuma sata.

Lauyan masu kara, Barista Abdullahi Tanko, ya shaida wa kotun cewa, wani mai suna Godday Jeremiah ne ya kai korafi ofishin ‘yan sanda na Bwari a ranar 23 ga watan Yuli.

Barista Tanko ya ce Mista Jeremiah ya yi karar ababen zargin ne kan yadda a yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Abuja da Lokoja, sai motar da ya hau ta lalace, lamarin da ya sa ta nemi wata motar a tashar Giri.

“Kwatsam sai suka loda jakunkunansa ba tare da izininsa ba a wata motar, inda suka bukaci ya biya su kudin aikin da suka yi masa.

“Sai ya ki amince wa bukatarsu, wanda a sanadiyar haka suka fara lakada masa duka kuma ana cikin haka ne aka sace masa waya kirar iphone 6, wadda darajarta ta kai N54,000.

Barista Tanko ya ce wannan laifin ya ci karo da sashe na 96, 264 da 288 na kundin laifuffuka, wanda kuma wadanda ake tuhumar duk suka musanta a gaban kotun.

Sai dai alkalin kotun, Sani Umar, ya bayar da belin wadanda ake tuhumar a kan kudi Naira 100,000 kan duk mutum daya tare da neman su gabatar da mutum guda-guda da zai tsaya musu.

Kazalika, alkalin ya ce dole ne wadanda za su tsaya musu su kasance mazauna yankin da kotun take da sannan su gabatar da fasfo na hoto guda biyu-biyu.

Alkalin kotun ya kuma ce idan wadanda ake tuhumar sun gaza cika sharuddan belin, to a ci gaba da tsare su a gidan yari na Suleja.

Aminiya ta ruwaito cewa alkalin ya dage sauraron karar zuwa ranar 28 ga watan Satumba.