✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 38 ne suka mutu a haɗarin jirgin sama a Kazakhstan

Mutane 67 ne ke cikin jirgin da suka haɗa da fasinjoji 62 da ma'aikatan jirgin biyar. Mutane 38 sun mutu, yayin da 29 suka jikkata

Jami’an ƙasar Kazakhstan sun bayyana cewa, mutum 38  ne suka mutu a haɗarin jirgin saman fasinja na Azerbaijan da ya afku a ranar Laraba a yankin yammacin ƙasar.

Hukumomin Azabaijan sun ce haɗarin jirgin sama ƙirar Embraer 190 ya afku a kusa da birnin Aktau, cibiyar mai da gas a gabashin gaɓar tekun Caspian.

A yayin da jirgin Azerbaijan ya ruwaito cewa mutane 67 ne ke cikin jirgin da suka haɗa da fasinjoji 62 da ma’aikatan jirgin biyar. Mutane 38 sun mutu, yayin da 29 suka jikkata, kamar yadda jami’an ƙasar suka tabbatar.

Jirgin dai ya taso ne daga Baku babban birnin Azabaijan da ke yammacin gaɓar tekun Caspian zuwa birnin Grozny na Chechnya a Kudancin Rasha.

“Wani jirgin sama da ke hanyarsa daga Baku zuwa Grozny ya yi haɗari a kusa da birnin Aktau. Mallakin jirgin saman Azerbaijan ne, “cewar Ma’aikatar Sufuri ta Kazakh a kan kafar Telegram.

Mataimakin Firaministan Ƙasar Kazakhstan, Kanat Bozumbayex, ya bayyana cewa an ceto mutane 29 da suka tsira da suka haɗa da yara biyu daga cikin tarkacen jirgin tare da wasu 11 daga cikin waɗanda suka tsira na cikin mawuyacin hali.

Jirgin saman Azerbaijan, ya dai yi saukar gaggawa a nisan kilomita uku (mil 1.9) daga Aktau.

Shugaban ƙasar Azabaijan Ilham Aliyex ya ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar makoki na ƙasa tare da soke ziyarar da ya shirya kaiwa ƙasar Rasha domin halartar wani taron shugabannin Ƙungiyar Ƙasashe Renon Ingila (CIS) wanda ya Ƙunshi tsoffin Ƙasashen Soviet.