✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 372 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa —NEMA

Muna kokarin samar da sabbin dabarun dakile wannan babban kalubale.

Rahotanni na nuna mutane 372 ne suka rasu sakamakon ambliyar ruwan sama da ta auku tsawon watanni takawas a Najeriya.

Babban Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Mustapha Habib Ahmed ne ya bayyana hakan a Abuja, yayin kaddamar da sababbin motoci da kayan aiki na musamman ga hukumar.

Ya ce jihohin da ambaliyar ta fi shafa sun hada da Adamawa da Jigawa da Kano da Bauchi da Neja da Anambra da kuma Ebonyi.

Idan za a iya tunawa dai a ranar Talata ne Gwamnatin Tarayya ta ce tun daga watan Janairu zuwa yanzu, ambaliyar da ta auku a jihohin Najeriya 22 da Abuja, ta yi sandiyar mutuwar mutane 115, da jikkatar 277,  yayin da gidaje 73,379 suka rushe.

To sai dai Darakatan a ranar Litinin ya ce: “ambaliyar ta mamaye jihohi 33 ne, birnin tarayya Abuja, kuma ta taba mutane sama da 508,000.

“Haka kuma ta yi sanadin mutuwar mutane kusan 372, da jikkatar mutane 277, da rugujewar gidaje kusan 37,633, da asarar dimbin dabbobi da gonaki da dama,” in ji shi.

Ya ce alamu na nuna idan aka cigaba da tafiya a wannan yanayin, ko shakka babu za a cigaba da samun karuwar rugujewar gine-gine, fashe-fashen tankar mai, da hadurran tituna da barkewar gobara.

“Saboda haka muna kokarin samar da sabbin dabarun dakile wannan babban kalubalen da hanyoyin ba da agajin gaggawa.”

“Za mu raba wadannan motoci ga ofisoshi NEMA da ke sassan Najeriya.”

Motocin dai sun hada da Motar kwana-kwana uku, da ta ba da agajin gaggawa uku, da kwale-kwalen zamani biyu, sai na jirgin ruwan ceto biyu.

Sauran sun hada da na`urar daukar hoto ta bincike 15, da na gano wurare 3, da sauran kayayyakin aiki.

%d bloggers like this: