Akalla fararen hula 35 ne suka mutu a yayin da ayarin motocin da ke dauke da kayayyaki a yankin Arewacin Burkino Faso ta taka wani bam da aka dasa, kamar yadda Gwamnan yankin ya tabbatar.
Fashewar, wacce ta raunata wasu mutum 37 ta faru ne a yayin da ayarin motocin da sojoji ke yi wa rakiyar a kan hanyar Bourzanga zuwa Djibo a ranar Litinin, inji Gwamnan Yankin Arewa maso Gabashin Sahel, Rodolphe Sorgo mai iyaka da Mali da Nijar.
- China ta fuskanci zafi mafi tsanani tun 1961
- LABARAN AMINIYA: Kungiyar Shugabannin Jami’o’in Najeriya Sun Kafa Kwamitin Sulhu Tsakanin Gwamnati da ASUU
Yankin da ke kan iyakoki uku ya kasance tsakiyar inda ake samun kalubalen tsaro da ke kara kamari a yankin sama da shekara 10 da suka gabata.
Kazalika, ana samun karuwar hare-hare daga kungiyoyin da ke da alaka da al-Qaeda da ISIL (ISIS) bayan mamayar da sojoji suka yi a Mali da Burkina Faso, a watan Mayu 2021 da Janairu 2022.
“Daya daga cikin motocin da ke dauke da fararen hula ta afka kan wani bam da aka dasa. Adadin wadanda suka mutu ya kai 35 tare da jikkata wasu 37, dukkansu fararen hula ne,” inji sanarwar Gwamnan yankin.
Sanarwar ta kara da cewa, “Masu rakiya cikin sauri sun tsare kewayan da abin ya shafa tare da daukar matakan taimaka wa wadanda abin ya ritsa da su.”
Wani mazaunin Djibo ya shaida wa Kamfanin Dilancin Labaran Faransa (AFP) cewa, “Motoci da dama, da suka hada da manyan motoci da motocin safa-safa na jama’a ne fashewar ta ritsa da su.
“Galibinsu ’yan kasuwa ne da za su sayi kayayyaki da kuma daliban da za su koma makaranta a Ouagadougou, babban birnin bayan hutun shekara,” inji mazaunin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasar.
Fashewar ta biyo bayan wasu jerin hare-hare da aka kai kan manyan titunan da ke shiga manyan biranen yankin da suka hada da Dori da Djibo.