Mutum 33 sun nutse a hatsarin kwalekwale da ke dauke da mutane 50 a Karamar Hukumar Lavun ta Jihar Neja.
Kwalekwalen ya kife da mutanen, ciki har da mata da kananan yara ne a ranar Juma’a da dare tsakanin kauyen Danchitagi na karamar hukumar da kauyen Gbara, Karamar Hukumar Mokwa.
- 2023: Atiku ya fara kamfe ta Fadar Sarkin Zazzau
- Dalibin likitancin da ke sana’ar abinci saboda yajin aikin ASUU ya rasu
Wani daga cikin masu aikin ceto ya ce, “Daga cikin mutum 50 da ke cikin kwalekwalen an ceto 17 da ransu, muna fargabar sauran ba su da rai saboda sun shafe awanni a mutane cikin ruwan — sai dai idan da wadanda suka iya ninkaya a cikinsu.
“Sannan ruwan wurin ya karu sosai saboda ruwan sama; muna dai yin iya kokarinmu don gano sauran,” in ji shi.
Ya bayyana cewa an garzaya da wadanda aka ceto da ransu zuwa asibitin kauye Gbara.
Mutanen da kwalekwalen ya kife da su sun fito ne bayan cin kasuwar Danchitagi da kuma wasu da ke dawowa daga bikin daurin aure a wani kauye da ke kusa da su.
Hatsarin, wanda aka danganta da ruwan sama da iska mai karfi da ya kuma yi sanadiyar asarar dukiya ta miliyoyin Naira.
Shaidu a yankin sun ce mutanen da suka yi hatsarin sun fito ne daga kauyukan muregi, Gbara, Gazhe, Tadima da sauransu.
Darakta-Janar na Hukumar Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Ahmed Ibrahim Inga, ya tabbatar da aukuwar hatsarin kwalekwalen, amma bai ba da adadin mutanen ba.
Ya ce hukumar ta fara aikin ceto a wurin da abin ya faru.
Shi ma Daga cin Gbara, Alhaji Mohammed Saba ya ce mutum 60 ne a kwalekwalen.