Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa, Dokta Emmanuel Akabe ya bayyana cewa mutum 300 sun kamu da cutar COVID-19 a jihar.
Ya sanar da hakan ne a yayin tattaunawarsa da hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa da bincike ta jihar.
- Gwamnatin Kano ta yi wa ‘yan jarida bita kan cutar Coronavirus
- Coronavirus: Za a fitar da almajirai 4,443 daga jihar Nasarawa
“Dole ne gwamanti ta tashi tsaye domin wayar da kan al’umma game da illar wannan cuta.
“Ina ba wa ma’aikatan lafiya shawara da su yi taka tsantsan wajen duba marasa lafiya, domin kare kansu daga kamuwa da cutar”, inji Akabe.
Akabe, wanda shi ne Shugaban kwamitin yaki da cutar a Jihar Nasarawa, ya ce wasu daga cikin ma’aikatan hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa ta jihar sun kamu da cutar.
Kamuwar mutum 300 da suka da coronavirus a shi ne adadi ma fi yawan da aka samu a jihar tun bayan bullar cutar a Najeriya.
Ya ja hankalin jama’a da su rika amfani da takunkumi, wanke hannu lokaci zuwa lokaci da kuma ba da tazara a cikin mutane.
Akabe ya ce gwamnatin jihar za ta shirya taron masu ruwa da tsaki domin lalubo hanyoyin wayar da kan jama’a.
Ya kara da cewa, a halin da ake ciki yanzu matasa na daga cikin wanda suka fi kamuwa da ita ba kamar yadda take a farko ba.