Wata mata da mijinta da kuma diyarsu mai shekara tara sun tsallake rijiya da baya, bayan motarsu ta yi adungure da su a kan babbar hanyar Abuja zuwa Lakwaja.
Rahotanni sun ce tayar motar da ke tafiya a guje ce ta fashe, nan take kuma motar ta fara kundumbala da karamar yarinyar da mahaifanta da ke ciki.
- Mahaifin tsohon gwamnan Kano Kwankwaso ya rasu
- Nan ba da jimawa ba Najeriya za ta fita daga matsin tattalin arziki – APC
Wani ganau ya ce bayan fashewar tayar sai motar, wacce ta taso daga hanyar Gwagwalada a yankin Babban Birnin Tarayya Abuja ta kwace wa direbanta, ta yi ta wuntsulawa akalla sau uku kafin ta fada a wani fili a gefen hanyar.
“A gaskiya Allah ne kawai Ya kiyaye iyalan wata motar ba ta biyo daya hannun ba, saboda bayan kifewar da ta yi sai da ta koma hannun da ba nata ba gaba daya,” inji shaidan.
Wakilin Aminiya wanda ya ziyarci wurin jim kadan da faruwar lamarin ya ce mai gidan matar wanda shi ke tuka motar, ya samu raunuka; kuma jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) sun kai shi asibiti.
Kwamandan FRSC na yankin Abaji, ACC Abubakar Shehu ya tabbatar da faruwar hatsarin a ranar Alhamis da misalin karfe 9:33 na safe.
Sai dai ya alakanta faruwar hatsarin da gudun wuce ka’ida da kuma fashewar taya.
Ya ce tuni aka garzaya da mutumin da ya samu rauni zuwa Babban Asibitin Abaji domin samun kulawa yayin da kuma suka dauke motar daga kan hanya.