Akalla mutum uku ne suka mutu bayan ambaliyar ruwa ta shafe babbar hanyar da ta hada Bauchi zuwa Kano a garin Kwanar Mulka da ke Karamar Hukumar Ningi ta Jihar Bauchi.
Wani ganau kuma mazaunin yankin na Kwanar Mulka, Ahmadu Abdullahi ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Juma’a sakamakon mamakon ruwan saman da aka tafka.
- DSS ta saki Yahudawan da ta kama bayan shafe kwana 20 a tsare
- ’Yan ISWAP 91 sun mika wuya ga sojoji a Borno
Ya ce ruwan ya sa kogin yankin ya cika makil sannan ya yi ambaliya wacce kuma ta yi sanadiyyar shafe babbar hanyar.
“Wata mota kirar bas dauke da mutum shida ta fada gefen hanyar da ruwan ya mamaye. Mata biyu daga cikin mutum shidan da ke cikin motar sun nitse yayin da sauran kuma aka ceto su.
“Har yanzu ba a gano gawar matan ba. Kazalika wani mutum shi ma ya nitse a kusa da gadar kuma ba a tsinto gawar shi ba,” inji Malam Ahmadu.
Kakakin ’yan sandan Jihar ta Bauchi, SP Ahmed Wakil ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce ba a sami asarar rai ko daya ba.
Ya kuma ce an ceto dukkan fasinjojin da ruwan ya ci.
SP Wakil ya kuma ce tuni jami’ansu suka yi wa hanyar kawanya domin kaucewa wata barnar a nan gaba.
Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Abubakar Y. Sulaiman wanda ya ziyarci wurin ya ce akwai ban tsoron a ciki.
Ya ce ambaliyar ta yi sanadiyyar raba mutanen Jihar ta Bauchi da makwabtanta na Jigawa da Kano.
Da yake bayyana wa kakakin yadda lamarin ya ritsa da shi, wani direba wanda shi ma ambaliyar ta shafa, Abubakar Abdullahi ya ce yana kan hanyarsa daga Kano zuwa Adamawa ne lokacin da ya ci karo da iftila’in.
Ya ce, “Akwai wasu motoci biyu ma da suka fada cikin rafin, an ceto mutum 11, amma biyu sun nitse, kuma har yanzu ba a samu an ceto su ba.”
Kakakin Majalisar, wanda kuma shine yake wakiltar mazabar ta Ningi a Majalisar Jihar ya ba da tallafin kudi ga wadanda ruwa ya ci motocinsu don su samu su karasa tafiyarsu, tare da yin addu’a ga wadanda suka rasu.
Wani mazaunin yankin, kuma shugaban Kungiyar Direbobin Tifa ta Ningi, Alhaji Ali Gadar Maiwa ya roki gwamnati da ta kawo musu agajin gaggawa ta hanyar gyara hanyar.