Matafiya uku ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu biyu suka samu raunuka a ranar Laraba, a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Wani mazaunin kauyen Kakau da ke kan titin Kaduna zuwa Abuja, Malam Nasir Idris, ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon gudun ganganci.
- Jihohi 34 za a iya samun rikici a lokacin zabe —Gidauniyar CLEEN
- Tsoffin kudi: Gwamnati ta bukaci Kotun Koli ta yi watsi da hukuncin da ta yanke
A cewarsa, hatsarin ya faru ne sakamakon fashewar tayar motar bas din ta yi sannan ta fada wani rami.
“Ina cikin gonata da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, kwatsam sai na ji karar hayaniya.
“Yayin da na garzaya wurin tare da wasu mutanen kauye, kura ta fara lullube ko’ina. Da kura ta lafa, sai muka hangi gawarwaki uku na kwance,” in ji shi.
Sai dai Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura a Jihar Kaduna, bai amsa kiran wayar da aka masa ba domin jin ta bakinsa kan faruwar hatsarin.