✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 3 sun mutu a hatsarin mota a Gombe

Muna ci gaba tattara bayanai domin gano musabbabin aukuwar hatsarin.

Wani mummunan hatsarin mota ya yi ajalin mutum uku a garin Ashaka da ke Karamar Hukumar Funakaye a Jihar Gombe.

Shugaban Hukumar Kiyaye Hadurra na Kasa reshen jihar, Felix Theman ne ya tabbatar da hakan yayin ganawa da wakilinmu ta wayar tarho.

Ya ce hatsarin ya faru ne da Yammacin Juma’ar nan yayin da wata babbar motar dakon kaya dauke da duwatsu da fadi a kusa da Gadar Bomala da ke garin Ashaka, lamarin da ya yi ajalin mutum uku nan take.

Ya ce yanzu haka mutum 3 ne suka tabbatar da mutuwarsu yayin da suke ci gaba da tattara bayanai don ganin dalilin faruwar hatsarin.

Bayanai sun ce hanyar wadda ta ratsa bayan gari dai ta zama tarkon mutuwa, la’akari da yadda ake yawan samun hatsarin mota a kai a kai da sanadiyyar rayuka.