✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 3 sun mutu, 12 sun jikkata a hatsarin mota a Ondo

An garzaya da wadanda suka ji rauni zuwa asibiti don ba su kulawa.

Akalla mutum uku sun mutu yayin da wasu 12 suka ji rauni a wani hatsarin mota a hanyar Akure zuwa Owo a Jihar Ondo.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) a jihar, Ezekiel Sonallah, ya tabbatar ya ce hatsarin rutsa da mutum 15; maza 12 da mata uku.

Ya ce  hatsarin da ya rutsa ne da wata mota kira Toyota Sienna mai lamba LND 778YG da kuma wata kirar bas mai lamba KTN 298YJ.

Aminiya ga gano hatsarin ya faru da misalin karfe 5: na safe daura da Makarantar Sakadaren ’Yan Mata ta Tarayya da ke jihar.

Sonallah ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon gudun ganganci, kuma tuni aka kai mutanen da suka ji rauni zuwa asibiti don ba su kulawar da ta dace.

Sannan ya yi kira ga fasinjoji su rika kai rahoton direbobin da ke tukin ganganci a yayin tafiye-tafiye ga FRSC don daukar mataki.

%d bloggers like this: