Mutum 23 suka rasu a wani hatsarin mota a kauyen Masha, kan titin Makera zuwa Mokwa da ke Karamar Hukumar Mashegu a Jihar Neja.
Wasu mutum 33 kuma sun samu raunuka daban-daban sakamakon harin motar.
- An yi garkuwa da mutum 17 a Jihar Neja
- Hadarin mota ya kashe mutum 15 da raunata 42 a Neja
- Hadarin mota ya kashe mutum 12 a Neja
- An cafke basarake a cikin ’yan bindiga a Neja
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta FRSC reshen Jihar, Joel Dagwa ya ce hatsarin na yammacin ranar Litinin ya ritsa ne da wata tirela ce, kirar DAF.
Ya ce bayan gudanar da bincike hukumar ta gano cewa gudun wuce kima ne ummulhaba’isin hatsarin, kuma direban motar da yaronsa sun tsere.
Rahoton ya bayyana cewar motar ta taso ne daga Jihar Kebbi dauke da shanu zuwa Jihar Legas.
Har wa yau, motar na dauke da mutum 55 maza a lokacin da hatsarin ya ritsa da su.
Ya ce dn dauke wadanda suka ji rauni zuwa Babban Asibitin Mokwa, inda a nan ne likitoci suka tabbatar ra rasuwar 23 daga cikinsu.