✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 22 sun kone a hadarin mota

Wani mummunan hadarin mota ya ci rayukan mutum 22 a kan hanyar Jahun zuwa Kiyawa a Jihar Jigawa sakamakon kwacewar da motar ta yi a…

Wani mummunan hadarin mota ya ci rayukan mutum 22 a kan hanyar Jahun zuwa Kiyawa a Jihar Jigawa sakamakon kwacewar da motar ta yi a Kwanar Jabarna da ke Karamar Hukumar Jahun.

Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa ta tabbatar da aukuwar hadarin ta bakin Kakakinta SP Audu Jinjiri, wanda ya ce motar ta kwace daga hannun direban ne a kokarinsa na kauce wa wani mutum da yake tsallaka titi, inda  ta bugi wasu jarkunan sayar da man fetur a gefen titi, kuma hakan ya sa wuta ta tashi, nan take motar ta kama da wuta hakan ya yi sanadiyar mutuwar dukkan wadanda suke cikin motar.

Motar mai lamba YD183HJA, an ce sunan direbanta Ayuba mai kimanin shekara 36, kuma dan asalin kauyen Ashafa da ke Karamar Hukumar Jahun ne wanda ya debo fasinjoji daga garin Jahun zuwa Kasuwar Shuwarin.

Direban da fasinjojinsa 21 babu wanda ya fita kuma babu wanda za a iya ganewa a cikinsu saboda  sun kone kurmus.

Daga cikin fasinjojin an gano maza 18 ne da mata biyar kuma an hada su an yi musu kabari daya bayan an yi musu Sallar Janaza kamar yadda Musulunci ya tanada.

SP Jinjiri ya kara da cewa ’yan sanda sun je wajen da al’amarin ya faru tare da likita wanda shi ne ya tabbatar da mutuwar wadanda suka kone kafin a yi musu jana’iza. Sannan ya kara da cewa ’yan sanda suna gudanar da bincike a kan lamarin.