✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 20 sun kone kurmus a hatsarin mota a Bauchi

Direben mota daya ya tsira da ransa a hatsarin da motoci biyu suka yi karo a Bauchi

Matafiya 20 ne suka kone kurmus a wani hatsari da ya ritsa da motocin haya biyu a kauyen Huturu da ke kan hanyar Bauchi zuwa Kano a ranar Talata.

Kwamandan Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) Reshen Jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya ce mutanen da hatsarin ya ritsa da su ’yan kasuwa ne a cikin wata mota kirar Golf 3, wadda ta yi karo da wata kirar Volkswagen Sharon.

Ya bayyana cewa mutum 21 ne a cikin motocin ’yan kasuwa, wadanda 20 daga cikinsu suka rasu, wani direba ya tsallake rijiya da baya.

Yusuf ya ce, “Hatsarin ya faru ne sakamakon gudun wuce ka’ida da kokarin wuce motor davke tafiya a gaba, da misalin karfe 11:30 na safiyar Talata a kauyen Huturu, dake kan hanyar Bauchi zuwa Kano.

“Mutanenmu sun samu rahoton ne da misalin karfe 11:38 na safe, cewa wani direba ya jikkata, fasinjoji 20 sun kone kurmus —maza 11, mata biyar, namiji daya da yara mata uku.

“An kai direban da ya ji rauni asibitin Kafin Madaki yayin da fasinjojin da suka mutu aka binne su kauyen Huturu.”

“Yusuf ya gargadi direbobin da su guji yin gudun wuce saa tare da yin tukin mota a tsaka-tsaki don kiyaye rayuwarsu da kuma lafiyar fasinjojin.