Aminiya ta tuntubi marubucin littafin tarihin Shata, Dokta Aliyu Ibrahim Kankara, malami a Sashen Nazarin Kimiyyar Duwatsu a Jami’ar Tarayya ta Dutsin-ma, wanda ya zayyano fitattun mutane 20 da ya tantance, wadanda kuma marigayi Mamman Shata ya yi masu waka:
1-Sarkin Daura Mamman Bashar: Ya san Shata tun 1948 a Bakori kuma ya yi masa wakoki har 13.
2-Bello Maitama Yusuf: Ya san Shata tun cikin 1972. Ya zama ubangidansa a 1979 kuma ya yi masa wakoki 71.
3-Usman Liman Durbi: Shi ne Hakimin Musawa (1939-1963). Ubangidan Shata ne tun a 1940 kuma ya yi masa wakoki da dama.
4-Inuwa Mammada Dan Sambo: Ya san Shata a 1940 kuma ubangidansa ne na farko. Ya yi masa waka guda daya amma tana da rassa.
5-Bawa Direba: Ya san Shata tun 1936 amma sai a 1947 ya yi masa waka, lokacin bikinsa a Katsina.
6-Umaru Danduna: Ya san Shata tun yana matashi amma sai a 1971 ya yi masa waka.
7-Sani Audi: Shata ya yi masa wakoki a 1950, a Batsari, lokacin yana Malamin Kada. Ya yi masa wata wakar 1970, lokacin yana aikin Kwastam.
8-Garkuwan Bauchi Amadun Kari: Ya san Shata a 1952, lokacin yana karatun Diploma kan Aikin Gona a Samaru Zariya. Sun san juna a Kano cikin 1963, lokacin Kari yana Sakataren Tafawa Balewa a Kano amma sai a 1971 ya yi masa waka.
9-Hauwa Mai Tuwo Matar Lado: Ta fara son Shata tun tana karama. Ya yi mata waka cikin 1976 a Kano.
10-Indo Kyaftin Zariya: Ta fara sanin Shata a watan Janairun 1943, a Zariya. Ya yi mata waka daya, ta ‘Haka nan ne Mamman…’ amma ya raba ta kashi-kashi.
11-Umaru Chiroman Gombe: Ya san Shata cikin 1966, a Gombe. Ya yi masa waka a shekarar. Da ya rasu ma ya yi masa wata wakar ta ta’aziyya a 1975.
12-Aliyu Lamidon Adamawa: Shata ya yi masa waka a 1979 a Yola.
13-Ja’e Dan Ali: Yana Mararrabar Daudawa kuma ya yi masa waka a 1975. Ya san Shata tun cikin 1970.
14-Haruna Dan Kasim: Ya kai Shata Makka cikin 1956, ya yi masa waka a 1955 a Kano.
15-Sufeto Yusufu Shema Dandoka: Ubangidan Shata na wani lokaci. Ya yi masa waka a 1955 a Katsina.
16-Kilishi Jikar Dikko: Shata ya yi mata waka a 1964, lokacin da ta auri Wamban Daura Bashar.
17-Alhaji Sani Store: Ubangidan Shata ne na lokaci mai tsawo. Ya yi masa wakoki uku a Katsina.
18-Hajiya Inno Ahmadu: Ya yi mata waka cikin 1974.
19-Alhaji Balan Goggo: Ya yi masa waka cikin 1965 a Katsina kuma ubangidansa ne na lokaci mai tsawo.
20-Wili Dan Usman Salgare: Ya san Shata cikin 1968 kuma ya yi masa wakoki kusan shida.