Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta cafke wasu maza biyu bisa zargin yi wa ƙananan yara mata fyaɗe a lokuta daban-daban a jihar.
Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce sun kama wani mutum mai shekara 47, da zargin yi wa ‘yar matarsa mai shekara biyu fyaɗe a Tudun Wada, Shamaki a ranar 5 ga watan Mayu.
- ’Yan bindiga sun kashe jarirai, sun bai wa karnuka namansu a Zamfara
- Da muna kan mulki ni da Lamido da mun ƙalubalanci Tinubu — Amaechi
Bayan samun rahoton daga matarsa, rundunar ’yan sandan ta garzaya gidansu inda ta kama wanda ake zargin, sannan suka kai yarinyar Asibitin Ƙwararru na Gombe domin duba lafiyarts.
Ya ce za a yi amfani da rahoton binciken asibitin a kotu.
Hakazalika, an kama wani mutum mai shekara 35 da ke unguwar Golkos a Ƙaramar Hukumar Billiri, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara shida fyaɗe a unguwar Awai.
Mahaifiyar yarinyar ce ta rahoton faruwar lamarin, inda ’yan sanda suka kama wanda ake zargin, sannan suka garzaya da da yarinyar Asibitin Kaltungo domin duba lafiyarta.
DSP Abdullahi ya ƙara da cewa rundunar ta kama wasu mutane 18 daban da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a faɗin jihar.