A ranar Lahadi an samu karin mutum 2 da suka mutu a Najeriya sakamakon cutar Coronavirus a yayin da mutum 964 suka kasance sabbin kamuwa da cutar.
Hakan na kunshe ne cikin alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Kasa NCDC ta fitar kamar yadda ta saba duk rana.
- Tilas PDP ta hada kai da APC wajen sauya fasalin Najeriya —Okechukwu
- Saraki ya gargadi Buhari kan rikicin Fulani da Yarbawa
- Gwamnatin Kaduna ta bude manyan makarantu
Alkaluman sun nuna an samu karin mutum 360 da suka kamu a Legas, sai mutum 88 a Abuja Legas da kuma karin mutum 73 a Jihar Ogun.
A Jihar Imo an samu mutum 72, sai Kaduna mai mutum 67 da kuma Filato mai mutum 57 yayin da aka samu mutum 41 a Abiya.
Cikin sa’a 24 an samu karin mutum mutum 41 a Osuna, da mutum 32 a Ribas sai mutum 26 da suka harbu a Jihar Kano.
Jihar Neja ta samu karin mutum 24, sai Binuwai na da mutum 23 da kuma mutum 20 a Edo, sai Kuros Riba mai mutum 20 yayin da kuma aka samu karin mutum 8 a Akwa Ibom da kuma mutum shida a Nasarawa.
Kazalika, an samu karin mutum shida sabbin kamuwa a kowane daya daga cikin Jihohin Zamfara da Ekiti sai kuma mutum hudu a Jigawa.
A jimilla yanzu, cutar Coronavirus ta harbi mutum 121,566 a fadin kasar tun bayan bullarta karon farko a watan Fabrairun 2020.
Kazalila, alkaluman na NCDC sun nuna cewa cutar ta kashe adadin mutum 1,487 yayin da tuni an salami mutum 96,501 bayan sun samu waraka.