Mutum biyu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin da ya auku a Akure, babban birnin Jihar Ondo.
Hatsarin ya faru ne da jijjifin safiyar Laraba bayan da wani dan acaba mai dauke da fasinjoji biyu ya yi gwabza wa wata babbar mota.
- Dan takarar Gwamnan Abiya na PDP ya rasu
- An gurfanar da matashin da aka kama da katinan zabe 29 a gaban kotun Kano
Majiyarmu ta ce, dan acaba ya dauki fasinjojin ne da nufin kai su asibiti inda suka gamu da iftila’in.
Hatsarin ya faru ne a yankin Oba-Ile cikin Karamar Hukumar Akure ta Arewa a jihar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito ana zargin rashin fitula a babur din da gudun wuce kima ne dalilan da suka haifar da hatsarin.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Olufunmilayo Odunlami-Omisanya, ya tabbatar da aukuwar hatsarin, inda ya ce an kwashi gawargwakin zuwa Asibitin Kwararru da ke Akure.