An tabbatar da rasuwar mutum 19, yayin da wasu takwas suka jikkata a wani hatsarin mota ranar Lahadi a kan hanyar ’Yangoji zuwa Gwagwalada da ke yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) mai kula da shiyyar Abuja, Dauda Biu, ne ya tabbatar da alkaluman ga Kamfanin Dillanci Labarai na Najeriya (NAN), lokacin da ziyarci wajen hatsarin.
- Amotekun za ta fara amfani da kudan-zuma da macizai wajen yaki da ta’ddanci a Oyo
- Kwalara ta barke a inda ake horar da tubabbun ’yan Boko Haram
Dauda ya ce hatsarin ya faru ne cikin tsakar-dare, bayan da wasu motoci uku – kirar Toyota Hiace masu lambobi MUB- 30 LG da DWR-985 XJ – da kuma wata mota da ke ajiye suka hadu da juna.
Kwamandan ya ce hatsarin ya ritsa ne da mutum 31, wadanda suka hada da maza 11 da mace daya, wadanda suka kone kurmus ta yadda ba a iya gane su.
Ya ce, “Daga cikin mutum 31 da hatsarin ya shafa, mutum takwas, da suka hada da maza bakwai da mace daya sun sami raunuka, mutum 19 kuma sun kone kurmus, ta yadda ba za a iya gane su ba.
“Binciken farko-farko ya nuna cewa babban makasudin hatsarin shi ne gudun wuce sa’a da kuma kokarin wuce wasu ababen hawan ba bisa ka’aida ba,” inji shi.
Dauda Biu ya ce Toyota Hiace din mai lamba MUB- 30 LG ta daki wata motar kirar Citroen ne, sannan ta kama da wuta ta kuma kashe ilahirin mutanen cikinta.
“Mota ta biyun kuma ta doki ta gaban ce sannan ita ma ta kama da wuta. Wutar ce ta kone motar ta biyu, wacce take dauke da lambar jihar Bauchi.
“Ta taso ne daga Takai a jihar Kano, za ta tafi Benin a jihar Edo. Ita kuma Citroen din wacce take dauke da kaji ta taso ne daga Zariya a jihar Kaduna a kan hanyarta ta zuwa Akwa Ibom.
“Daga bisani ma’aikatan ceto sun sami damar ciro gawarwakin daga cikin motocin,” inji shi.
Ya kuma ce tuni ’yan sanda suka karbi ragamar binciken musabbabin hatsarin da kuma yadda za a yi wa gawarwakin da suka kone din jana’iza ta bai-daya.
Dauda Biu ya kuma ce babu damar adana gawarwakin har a gano masu su saoba sun yi konewar da ba za a iya gane su ba.
Ya kuma ce wadanda suka jikkata an garzaya da su wani asibiti da ke Kwali a Abuja, yayin da wata gawa guda daya kuma da aka iya gane ta aka adana ta a dakin adana gawarwaki na Babban Asibitin Kwali. (NAN)