✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 189 sun kamu da Kwalara a kananan hukumomi 20 a Kano

Mutum biyar sun rasu daga cikin 189 da suka kamu da cutar amai da gudawa a Kano.

Akalla mutum 189 ne suka kamu da cutar amai da gudawa, wato Kwalara a kananan hukumomi 20 a Jihar Kano.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Talata.

Ya ce, 184 daga cikin wadanda suka kamu da cutar sun warke, biyar sun mutu, kuma a yanzu jihar ba ta samu bullar cutar ba sakamakon hadin gwiwar jama’a daban-daban na jihar.

A cewarsa, Cibiyar Dakile Cututtuka ta Kasa (NCDC), ta samu mutum 2,339 da suka kamu da cutar ta Kwalara a cikin fiye da jihohi 30 daga watan Janairu zuwa Yunin 2022.

Ya kara da cewa har yanzu Najeriya na fama da cutar Kwalara musamman a lokacin damina saboda rashin tsaftar muhalli, rashin kula da shara a gida da kuma yin bayan gida a fili, wanda a cewarsa su ke taimakawa wajen yada kwayoyin cutar.

Kwamishinan ya bada tabbacin ci gaba da jajircewar gwamnati wajen samar da isassun kayan aiki na kiwon lafiya ga mutanen jihar domin kawar da barkewar cutar ta Kwalara da sauran cututtuka tare da yin kira ga jama’a da su tabbatar da tsaftar jikinsu da ta muhalli.