Rundunar ’Yan Sandar Jihar Bauchi ta ce mutum 18 sun rasa rayuwarsu sakamakon nutsewar kwale-kwale a kogi Buji na karamar hukumar Itas Gadau ta jihar Bauchi.
Kakakin Rundunar, Ahmed Mohammed Wakil ne ya bayyana haka a takardar da ya raba wa manema labarai.
- Amarya da mahaifiyarta sun mutu a hatsarin kwalekwale
- Dalilin da kwale-kwale ya hallaka mutum 7 a Nasarawa
- Mutum 11 sun mutum a kifewar kwale-kwale a Ogun
“An tsamo gawarwakin daga cikin ruwa aka kai su Babban Asibitin garin Itas domin tantance abin da ya kashe su.
“Likita ya tabbatar da mutuwar mutum 18 tare da ceto mutum biyar”, kamar yadda takardar ta kumsa.
Kakakin ’yan sandan ya ce daga cikin wadanda suka rasun akwai yara 16 da manya biyu.
Ya ce kwalekwalen na dauke da manoma 23 ne lokacin da hatsarin ya auku, kuma an yi nasarar ceto mutum 5 amma har yanzu mai tukin kwalekwale da wani mutum daya ba su san inda kansu yake ba.
“Wadanda suka rasu sun hada da: Abdulraham Shehu, Suwaiba Yusuf, Saude Abdulkarim, Fatima Maigari, Zuwaira Maigari, Hari Maigari, Hussaina Maigari, Ummani Abdulkarim da kuma Halima Saminu.
“Sauran sun hada da: Naja’atu Hamza, Nura Abdullahi, Yahuza Abdullahi, Hafsa Abdullahi, Sadiya Hashimu, Khadija Alhassan, Amina Idris, Kaltime Hudu, da kuma Furaira Malam Magaji”.