Mutum 15 sun rasu, wasu da dama kuma sun bace sakamakon hatsarin kwalekwale gabanin shan ruwa a Jihar Neja.
Mutum 17 kuma sun tsallake rijiya a hatsarin kwalekwalen da ya auku da magaribar ranar Asabar a yayin da mutanen ke hanyar komawa gida bayan cin kasuwa.
- Sallah: Ranar Talata za a fara neman wata —Sarkin Musulmi
- ’Yan bindiga sun sa cikina ya zube —Dalibar Afaka
- An fitar da sunayen wadanda za a dauka aikin NDLEA
Hatsarin ya ritsa da mutanen ne bayan sun baro Kasuwar Zumba a Karamar Hukumar Shiroro za su koma gidajensu a Tijana da ke Karamar Hukumar Munya, Jihar Neja.
Sarkin Kasuwan Zumba, Malam Adamu Ahmed ya ce kwalekwalen na dauke da mutun 60 da suka hada da mata da kanana yara a lokacin da ya kife sakamakon iska mai karfi.
Ya cewa wasu daga cikin mutanen na hanyarsu ta komawa gidajensu da suka kaurace wa ne a kwanakin baya saboda hare-haren ’yan bindiga.
Malam Adamu ya ce masu ninkaya sun yi nasarar ceto mutum 17 a raye, kasancewar ba a jima da faruwar lamarin ba aka sanar da su.
Suna kuma ci gaba da kokarin ceto mutanen da ba a gani ba, duk da cewa ana ruwan sama kamar da bakin kwarya a lokacin da muke kammala hada wannan rahoto.
A shekarar 2017, kifewar wani kwalekwale ya lakume rayuka 13 daga cikin fasinjojinsa mutum 30 a hanyarsu ta komawa gida daga kasuwar ta Zumba.