Akalla mutum 146 ne suka rasu, wasu 150 kuma suka samu raunuka a wani turereniya da aka samu a wurin biki a birnin Seoul na kasar Koriya ta Kudu.
Mace-macen sun auku ne a lokacin da mutane suka yi turereniyar ana tsaka da bikin Holoween, wanda ya tara dimbin mutane a wani tsukakken layi a birnin.
- ’Yan daba sun kai wa masu zagayen Mauludi hari a Neja
- Bankin CBN da NIRSAL sun soma kwato bashin da suka bayar
Wasu daga cikin wadanda suka samu rauni suna cikin mawuyacin hali, kuma Shugaban Hukumar Kashe Gobara na yankin Yongsan, Mista Choi Seoung-Beom, ya bayyana cewa akwai yiwuwar adadin wadanda suka rasu zai karu daga 146.
A cewarsa, an tura ma’aikatan ceto sama da 400 da motoci 140 domin gudanar da aikin agaji da jinyar wadanda suka samu rauni bayan faruwar lamarin a ranar Asabar.
Rahotanni sun nuna turereniyar ta fara ne a lokacin da mahalarta taron suka yi ta kokarin kurdawa su yi gaba a tsukakken layin, bayan adadin mahalarta ya yi ta karuwa har ya kai Dubai.
Wannan turereniya ta auku ne kusa da otel din Hamilton, wanda ya shahara da yin casu a birnin na Seoul.
Karin farko ke nan da ake gudanar da bikin Haloween tun bayan bullar cutar COVID-19, wadda ta sa aka kafa dokar bayar da tazara da haramta gudanar da taruka.