Wani hatsarin mota da ya auku a yankin Ipetu-Ijesha na Jihar Osun da yammacin ranar Asabar ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 14.
Hatsarin dai ya ritsa da wata mota ne kirar Sienna mai ruwan kasa mai dauke da lambar KRD 842 GY, da kuma wata A-kori-kura mai lambar BAU 171 ZE.
- Cutar Kwalara ta kashe mutum 54, ta kama 604 a Abuja
- Akwai yarjejeniyar Buhari zai mika mulki ga Tinubu a 2023 – Sanata Hanga
Wadanda suka mutun sun hada da wasu yara mata su biyu, maza yara guda hudu, maza manya su hudu, sai kuma wasu manyan mata suma su hudu.
Jami’an Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) wadanda suka yi wa wurin kawanya tuni suka kwashe wadanda suka sami raunuka zuwa asibiti, yayin da su kuma wadanda suka mutu aka kai su dakin adana gawarwaki.
Kwamandan shiyya na hukumar ta FRSC a Jihar, Kwamanda Paul Okpe ya ce akwai yuwuwar yunkurin daya daga cikin motocin na wuce ’yar uwarta ne ya haddasa hatsarin.
Paul, wanda ya yi magana ta bakin kakakin hukumar a Jihar, Misis Agness Ogungbemi ya ce an garzaya da gawarwakin wadanda suka mutun zuwa sashen adana gawarwaki na Asibitin Wesley da ke garin Ilesa.