Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC), ta ce an samu karin mutum 1,368 da suka harbu da cutar COVID-19 a ranar Litinin.
Daga cikin wadanda suka kamu, Jihar Legas ita ce ke kan gaba da mutum 844, sai Birnin Tarayya, Abuja, mutum 209, yayin da Jihar Oyo ke da mutum 58, sai Abiya mai 51.
- ’Yan daba sun kai wa Shugaban Jami’ar OAU da ke Ile-Ife hari a cikin makarantarsa
- COVID-19: Mutum 3 sun mutu sanadiyyar daskarewar jini bayan karbar rigakafin Pfizer
A Ondo mutum 39 ne suka kamu, Ogun na da 30, Kaduna 26, Delta na da mutum 20, Akwa Ibom 17, Osun 15, sai Jihar Ekiti mai mutum 12.
A Anambra an samu mutum bakwai, Jihar Zamfara ita ma na da mutum bakwai, sai Kuros Riba mutum shida.
Adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya tun bayan bullarta ya kai 225,255 amma an yi nasarar sallamar mutum 211,660 daga cibiyoyin killace masu cutar.
Yawan wadanda suka rasa rayukansu a sanadin COVID-19 ya kai 2,985.
NCDC ta jadadda muhimmancin bin matakan kariyar COVID-19 tare da karbar allurar rigakafinta a tsakanin al’umma.