✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 1,204 sun kamu da cutar Coronavirus a Najeriya – NCDC

Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta sanar cewa a ranar Litinin an samu mutum 1,204 sabbin kamuwa da cutar Coronavirus a fadin…

Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta sanar cewa a ranar Litinin an samu mutum 1,204 sabbin kamuwa da cutar Coronavirus a fadin Najeriya.

Sanarwar hakan na dauke ne a kan allon taskar bayanai mai dauke da alkaluman da suka shafi cutar Coronavirus na Hukumar NCDC da ke shafinta na yanar gizo.

Alkaluman sun nuna cewa Jihar Legas ta samu kaso mafi yawa na wadanda suka kamu da cutar cikin sa’a 24 da mutum 654 sai kuma Abuja, babban birnin kasar da mutum 200.

Sauran Jihohin da aka samu sabbin kamuwar sun hadar da; Filato (60), Kaduna (54), Kano (40), Ribas (30), Edo (28), Nasarawa (25), Kebbi (19), Bauchi (18), Oyo (13), Akwa Ibom (12), Bayelsa(11), Ogun (11), Delta (9), Abia (8), Benue(5), Imo (3), Borno (2), Sakkwato (1) da Osun (1).

Ya zuwa yanzu jimillar wadanda cutar ta harba a fadin kasar tun bayan bullarta karon fari a watan Fabrairun 2020 sun kai 91,351, yayin da tuni mutum 75,699 sun warke sai kuma mutum 1,318 da suka riga mu gidan gaskiya a sakamakon cutar.