✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 12 sun rasu a hatsarin mota a Ebonyi

Kwamandan FRSC a Jihar ta tabbatar da faruwar hatsarin.

Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) ta tabbatar da mutuwar fasinjoji 12 a wani hatsarin mota da ya auku a Jihar Ebonyi.

Kwamandan hukumar a jihar, Uche Chukwurah ta shaida wa ’yan jarida a Abakaliki cewa hatsarin ya auku ne tsakanin wata bas da wata mota kirar Honda ranar Talata atitin Ezillo da ke babbar hanyar Enugu zuwa Abakaliki-Ogoja.

Wani ganau da ya zanta da Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya ce motocin sun yi karo ne a lokacin da suke tsaka da gudun wuce kima.

Kwamandar FRSC ta jihar, Uche Chukwura , ta ce, “Lambar bas din ita ce EBJ 350 XA, daya motar kuma ba ta da lamba.

“Mutum 14 ne hatsarin ya rutsa da su, inda 12 suka mutu, biyu kuma suka samu munanan raunuka.

“Wadanda suka mutu sun hada da maza 10 da mata biyu, kuma hatsarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safe,” in ji ta.

Kwamandar ta ce an kai fasinjojin da suka jikkata asibitin koyarwa na tarayya na Alex-Ekwueme da ke a Abakaliki domin yi musu magani.

“Hukumar FRSC na jajanta wa iyalan wadanda suka mutu tare da yi musu addu’ar Allah Ya jikansu.

“Muna kira ga masu ababen hawa da su gane cewa rai guda daya ne,” in ji ta.