✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 12 sun mutu a hatsarin mota a Kwara

Hatsarin ya faru ne lokacin da direban Hiace din yake tsala gudu a hannun da ba nasa ba.

Akalla mutum 12 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya faru a kan hanyar Ilorin zuwa Ogbomosho da ke Jihar Kwara a ranar Asabar.

Rahotanni sun ce wata mota kirar Toyota Hiace mai cin mutum 18 da ke hanyar zuwa Legas ce ta yi taho-mu-gama da wata babbar mota kirar Daf.

Fasinjoji shida dai da suka tsira da ransu sun ji raunuka daban-daban a hatsarin da ya faru wajen misalin karfe 7:00 na safe.

Wani ganau ya ce hatsarin ya faru ne lokacin da direban Hiace din yake tsala gudu a hannun da ba nasa ba.

Kwamandan Shiyya na Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar ta Kwara, Jonathan Owoade, ya tabbatar wa wakilinmu faruwar hatsarin.