Akalla mutane 12 ne suka mutu, wasu akalla 500 suka jikkata a ranar Asabar a wani turmutsitsin da aka yi a filin wasan kwallon kafa a kasar El Salvador.
Carlos Fuentes, kakakin kungiyar agajin gaggawa ta Comandos de Salvamento, ya ce suna jinyar fiye da mutane 500 da turmutsutsin ya ritsa da su.
Hukumomin kasar sun alakanta lamarin da yadda magoya baya suka yi ta turereniyar shiga filin wasa na Cuscatlan da birnin San Salvador, hedikwatar kasar, domin kallon wasan cikin gida tsakanin kungiyoyin Alianza da FAS.
An dakatar da wasan, yayin da jami’an agajin gaggawa suka kwashe mutane daga filin wasan, inda daruruwan ‘yan sanda da sojoji da motocin daukar marasa lafiya suke taimakawa.
Daraktan ‘yan sandan farar hula (PNC) Mauricio Arriaza ya tabbatar da mutuwar mutane 12, inda ya ce, “Harkar kwallon kafa na birnin Salvador na cikin makoki.”
Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) Gianni Infantino ya jajanta wa iyalai da abokanan wadanda lamarin ya rutsa da su, inda ya kira turmutsutsun da abin takaici.
Daga cikin wadanda suka tsira, Sandra Guzman, ‘yar shekara 40, wadda aka sallama daga asibiti da sanyin safiyar Lahadi da bandeji a gwiwarta, tare da kawarta, Javier Ramirez, 31, sun ce wannan shi ne “na farko da na karshe” saboda ba za su koma filin wasa ba.
Ministan lafiya Francisco Alabi ya fada a baya cewa cibiyar sadarwa ta asibitocin kasar tana ba da kulawar jinya ga dukkan marasa lafiya.