✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 12 sun bakunci lahira a hanyar Kaduna zuwa Abuja, 25 sun jikkata

Mutum 12 ne ajali ya katse masu hanzari a wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da su ranar Laraba a kan babbar hanyar Kaduna…

Mutum 12 ne ajali ya katse masu hanzari a wani mummunan hatsarin mota da ya ritsa da su ranar Laraba a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Aminiya ta samu cewa wasu mutum 25 sun jikkata inda a halin yanzu suke samun kulawa a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Haka kuma dabbobin kiwo da dama sun salwanta a mummunan hatsarin da ya auku.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya ce hatsayin ya auku bayan wata babbar motar daukan kaya ta kwace wa direbanta saboda rashin kyawun hanya da kuma gudun da ya wuce kima.

“Wannan shi ne dalilin da ya sanya tirelar ta kauce daga kan hanya kuma ta kuma kife wanda a sanadiyar haka mutum 12 suka mutu yayin wasu mutum 25 suka ji rauni,” inji Aruwan.

Kwamishinan ya jagorancin tawagar jami’an tsaro wajen gudanar da sintiri a kan babbar hanyar ta Kaduna zuwa Abuja domin tabbatar da kiyaye dokokin tuki.

Ya ce Gwamna Nasir El-Rufa ya bayyana damuwarsa bayan samun rahoton hatsarin, ya kuma jajanta wa ’yan uwan mamatan da kuma yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki.

Aruwan ya ce Gwamnan ya kuma gargadi matafiya masu amfani da  babbar hanyar da su guji saba ka’idodin tuki musamman gudun da ya wuce kima, tukin gaganci, da yin lodi fiye da kima.