Rahotanni daga Philippines sun nuna akalla mutum 110 sun mutu sannan sama da miliyan 2.4 sun shiga matsi sakamakon iftila’in ambaliyar ruwa da gocewar kasa da ta auku a kasar.
Hukumar kula da iftila’i ta kasar ta fada a ranar Talata cewa, ambaliya da gocewar kasar sun faru ne sakamakon mamakon ruwan sama.
- Duk da ambaliyar ruwa, babu barazanar karancin abinci a Najeriya – Minista
- Yadda ake bude makarantun kudi a Kwara abin damuwa ne – Majalisa
A cewar hukumar, ana ci gaba da neman wasu mutum 33 da suka bace, yayin da sama da mutum 100 sun jikkata.
Ta kara da cewa, iftila’in ya lalata gidaje sama da 100 a yankin Magundanao da ke Kudancin kasar, kuma 59 daga cikin wadanda suka mutun daga yankin suke.
Kazalika, hukumar ta ce mutum 16 sun bace a Maguindanao, tare da cewa mawuyacin al’amari ne a gano masu sauran numafashi daga wadanda lamarin ya rutsa da su a yankin.
Sauran yankunan da lamarin ya shafa kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana sun hada da Yammacin Visayas da Cavite da Laguna da kuma Batangas.