✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 11 sun mutu, 22 sun ji rauni a hatsarin mota

An garzaya da ragowar wanda suka ji rauni zuwa asibiti.

Mutum 11 sun bakunci lahira yayin da 22 ciki har da mata biyu suka ji rauni a wani hatsarin mota da ya ritsa da su a Gbangan a Jihar Osun.

Hatsarin ya faru ne kusa da Sakatariyar Karamar Hukumar Ayedaade, wadda ta ke da tazarar kilomita biyar daga Gadar Osogbo zuwa Ibadan.

  1. An bankado sansanonin horon sojin kungiyar IPOB
  2. Shan kwaya: NDLEA ta cafke mutum 363 a Jigawa

Hatsarin ya faru tsakanin wata motar haya kirar Mazda E2000 da kuma wata mota kirar Toyota Hiace.

Jami’an Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen jihar sun kai dauki wajen da hatsarin ya faru tare da kai wadanda suka ji rauni zuwa asibiti.

Kwamandan Hukumar a Jihar, Paul Okpe, ya tabbatar da faruwar hatsarin.

Okpe ta hannun kakakin hukumar, Misis Agness Ogungbemi, ya ce hatsarin ya faru ne sakamakon taho-mu-gama da ababen hawan suka yi.

Kazalika, ya ce an samu wayoyin hannu da kayayyaki a wurin da hatsarin ya faru, kuma an mika su ga ’yan sanda don gudanar da bincike.

“An kai mutum 16 asibitin Ariremako a Gbongan, wasu shida kuma an kai su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Awolowo (OAUTH), da ke Ile-Ife,” cewarsa.

’Yan uwan wanda suka rasu sun dauki gawarwakinsu don yi musu sutura.