✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 11 sun kamu bayan kwana 5 babu COVID-19 a Sokoto

Cutar coronavirus ta kama mutum 11 a jihar Sokoto kwana biyar bayan sallamar ragowar masu ita a jihar.  Sabbin masu cutar na daga cikin almajirai…

Cutar coronavirus ta kama mutum 11 a jihar Sokoto kwana biyar bayan sallamar ragowar masu ita a jihar. 

Sabbin masu cutar na daga cikin almajirai 33 ‘yan asalin jihar Sokoto da aka mayar da su daga jihar Kaduna a ranar 4 ga watan Yuni.

Kwamitin yaki da cutar coronavirus a jihar Sokoto ya ce an gano almajiran na dauke da cutar ne tun kafin a mika su ga iyayensu.

“An killace almajiran su 33 a Sansanin Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC) da ke Wamakko.

“Bayan isowarsu ne aka yi musu gwajin cutar wadda aka samu 11 daga cikinsu na dauke da ita”, inji sanarwar.

Ta kara da cewa Gwamanatin Jihar za ta yi aiki da takwararta ta Jihar Kaduna wajen gano mutanen da yaran suka yi mu’amala da su a makarantarsu da ke Zaria, inda daga nan aka mayar da su Sokoto.