✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 11 aka kashe don tabbatar da dokar zaman gida

A wani rahoto da Hukumar kare hakkin bila’adama ta kasa ta sanar na cewa, akalla mutum 11 ne aka kashe ba bisa ka’ida ba a…

A wani rahoto da Hukumar kare hakkin bila’adama ta kasa ta sanar na cewa, akalla mutum 11 ne aka kashe ba bisa ka’ida ba a cikin makonni uku da sanya dokar zaman gida a shirin dakile yaduwar cutar Coronavirus a Najeriya.

A cewar rahoton, jihar Abia ita ce ke kan gaba a jihohin da lamarin ya fi kamari, inda aka hallaka mutum hudu.

Tunda farko dai wani rahoto da hukumar ta fitar ya nuna cewa, a makonni biyu na farkon sanya dokar, jami’an tsaron Najeriya sun yi sanadiyyar mutuwar akalla mutum 18 a yunkurinsu na ganin sun tabbatar da bin dokar, alkaluman da a wancan lokacin suka haura na wadanda cutar ta hallaka.

Korafe-korafen da hukumar ta samu

Hukumar kare hakkin bila’adama ta kasa, ta ce ta karbi akalla korafe-korafe 104 a kan batutuwan da suka shafi take hakkin bil’adama a makonni ukun da aka kara tsawaita dokar tilasta zaman gidan.

Shugaban hukumar, Barista Tony Ojukwu wanda ya bayyana haka a wata sanarwa ya kara da cewa baya ga jihar Abia, a jihar Delta mutum biyu aka hallaka, a yayin da kuma a jihohin Neja da Jigawa da Legas, Anambra da Ribas mutum dai-dai ne aka hallaka.

Barista Tony Ojukwu ya kara da cewa, a cikin mutum 11, ‘yan sanda sun yi sanadiyyar mutuwar mutum bakwai, yayin da kuma jami’an hukumar tsaro ta farin kaya sibil defens NSCDC, hukumomin tsaro na jihohi da kuma kwamitin yaki da cutar na jihar Abia kuma suka yi sanadiyyar mutum dai-daya kowannensu.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, shugaban hukumar Ojukwu ya ce suna ci gaba da bincike don gano wanda yake da hannu wajen kisan da ya faru a jihar Jigawa.

Laifuka

Bayan batun hallaka mutane, sauran laifukan da rahoton ya ambata sun hada da: Zargin azabtarwa da muzgunawa jama’a guda 34, take ‘yancin dan’adam, kamawa da tsarewa ba bisa ka’ida ba guda 14, kwace kayan mutane guda 11, yayin da kuma korafe-korafe guda 15 da suke da alaka da cin zarafin mata.

A sabon rahoton wanda ya gudanar da bincike daga ranar 13 ga watan Afrilu zuwa 4 ga watan Mayu, ya ce an samu raguwar kisan tun bayan rahoton farko da hukumar ta fitar a makonni ukun farko na sanya dokar hana fitar, a inda tace an sami akalla zargin take hakkin bil’adama har guda 105 daga ranar 30 ga watan Maris zuwa 13 ga watan Afrilu 2020.

Jihohin da aka samu korafi

Rahoton ya ce, hukumar ta karbi korafe-korafen ne a jihohi 26 daga cikin 36 tare da yankin babban birnin tarayya Abuja.

Jihohin sun hada da: Abia da Adamawa da Akwa Ibom da Kano da Jigawa da Kuros Ribas da Ebonyi da Edo da Enugu da Ekiti da Delta da Imo da Legas, Nasarawa da Neja da Ogun da Osun da Borno, Bayelsav da Kogi da Benuwe da Anambra da Kaduna, Gombe da Zamfara da kuma Ribas.

Rahoton korafe-korafe

Yayin da yake bayar da alkaluman rahoton, Ojukwu ya ce hukumar tasa ta karbi korafe korafe guda 49 a makon farko na tsawaita dokar hana fita, 33 a mako na biyu sai kuma guda 23 a mako na ukun.

Ya kara da cewa, raguwar da aka samu a adadin ya nuna cewa an samu ci gaba sosai bisa yadda ake zargin jami’an tsaro na gwamnatin tarayya da ma na johohi da wuce-gona-da-iri wajen tilasta jama’a su bi dokar zama a gidan.

Ci gaban da aka samu

Ojukwu, ya kuma kara da cewa ci gaban da aka samu yana da nasaba da jajircewar da hukumarsa tayi wajen wayar da kan jama’a biyo bayan rahotan da ta fitar ranar 14 ga watan Afrilu, hadi da kokarin jami’an tsaron wajen ganin sun rage yawan muzgunawa mutanen.

Sai dai ya yi takaicin cewar jihar Enugu ita ce ke kan gaba wajen laifukan a yayin da take da guda 13, yayin da jihar Imo ke biye mata baya da guda 12 kamar yadda rahoton ya nuna.

Hakazalika hukumar ta karbi korafe-korafe har guda 10 a jihohin Akwa Ibom da Nasarawa, sai kuma Abiya da Delta dak e da kowaccen su take da guda.

A jihar Legas kuwa, rahoton ya ce korafe-korafe guda biyar kacal aka samu, wanda hakan ke nuna an sami ragi daga guda 28 din da aka samu a rahoton farkon.

A yankin babban birnin tarayya Abuja da jihar Benuwe kuwa an samu rahoton zargin take hakkin har guda hudu, sai kuma jihohin: Neja, Zamfara, Osun da Ribas da aka samu guda uku a kowaccen su.