✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Jigawa

Motocin biyu sun yi gaba da gaba da juna, lamarin da ya haddasa hatsarin.

Akalla mutum 10 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya auku a garin Kwanar Gujungu da ke Karamar Hukumar Taura da ke Jihar Jigawa.

ASP Lawan Shiisu, kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ya ce motoci biyu; Honda mai lamba NSR 469 AE, da Golf mai lambarm Auy 292 XA ne suka yi da gaba-da-gaba.

Shiisu, ya ce Honda din na dauke da fasinjoji biyar, yayin da Golf din take dauke da fasinjoji hudu.

“A ranar Asabar, da misalin karfe 12:00 na safe, wani mummunan hatsarin mota da ya yi sanadin mutuwar mutum 11 a garin Kwanar Gujungu, lokacin da motoci biyu suka yi karo da juna.

“Sakamakon haka duka mutum 10 da ke cikin motocin biyu sun rasu,” in ji shi.

Ya ce tawagar ‘yan sanda daga babban Ofishinsu da ke Taura, ta garzaya zuwa wurin inda suka kai wadanda abin ya shafa zuwa babban asibitin, Taura, inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsu.

“Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ahmadu Abdullahi, ya aike ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan.

“Ya yi addu’a Allah Madaukakin Sarki da Ya yi musu rahama, Ya gafarta musu kurakurensu,” in ji Shiisu.