Hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna sun tabbatar da rasuwar mutum 15 da raunata 24 yayin da wasu ‘yan bindiga suka kai wani sabon hari a garin Ungwan Pah II da ke unguwar Gwandara a karamar hukumar Jama’a jihar Kaduna.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar DSP Yakubu Sabo ya bayyana wa majiyarmu hakan.
Sabo ya ce, a yanzu haka Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ahmad Abdulrahman ya bayar da umarnin a binciko wadanda suke da alhakin kai harin a yankunan.