Masu aikin cewa sun tabbatar da mutuwar mutum 10 wasu mutum hudu kuma sun bace a wani hadain jirgin ruwa a jihar Legas.
Hukumar kula da ruwa na cikin gida a jihar Lagas (LASWA) ta tsamo gawarwaki 10 da suka hada da mace daya, sannan ta ceci mutum hudu a raye.
“An tabbatar da mutuwar mutum 10 wasu hudu kuma ba a gan su ba”, inji shugaban LASWA Oluwadamilola Emmanuel a cikin wata sanarwa.
Oluwadamilola Emmanuel ya ce igiyar ruwa ce ta kifar da jirgin fasinjan, kafin fasinjoji su gama sanya rigunansu na ninkaya.
Ya ce wani wanda ya tsira ya ce hatsarin ya faru ne a lokacin da matukin jirgin yake kokarin kudade daga wurin fasinjoji, har hankalinsa ya dauke.
LASWA ta ce mutum 19 ne ke cikin jirgin ruwan sadda ya yi hatsarin a hanyarsa ta zuwa Kirikiri daga Badagry.
Hatsarin na ranar Laraba 29 ga wata shi ne irinsa na biyu da ya salwantar da rayuka a wata Yuli.
A ranar uku ga watan na Yuli mutum bakwai sun mutu bayan jirgin da suke ciki mai dauke da mutum 21 daga Ebute-Ero zuwa Ikorodu ya yi hatsari.
Gabanin kifewar jirgin ruwan na ranar Laraba wani jirgi ya yi hatsari a hanyarsa ta zuwa Ikoyi daga Ilashe, amma an kubutar da mutum goma da yake dauke da su.