Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ne ke kan gaba a yawan kuri’u a zaben kasar da aka yi ranar Talata.
Alkalumman da hukumar zaben kasar ta fitar sun nuna cewa kawo yanzu an kidaya kashi 3/4 na yawan kuri’un da aka jefa kuma Shugaba Kenyatta ya samu kashi 55% daga cikinsu; yayin da babban abokin hammayarsa, Raila Odinga, ya samu kashi 44% kamar yadda BBC ta ruwaito.
Sai dai tuni da kawance ‘yan hammaya ya yi fatali da sakamakon zaben, yana mai cewa turawan zaben ba su nuna takardun sakamakon zaben da za su tabbatar da sahihanci sakamakon da suka bayar ba.
‘’Wadannan alkalumman na shaci-fadi ne, na bogi ne,’’ in ji jagoran kawancen adawar Raila Odinga.
Hukumar zaben kasar da ta yi kira ga ‘yan kasar da su kwantar da hankulansu su jira cikakkaken sakamakon zaben cikin tsanaki.
Mutane a ciki da wajen kasar dai na fargabar sake barkewar rikicin bayan zabe a kasar irin wanda aka yi a shekara ta 2007 lokacin da aka kashe mutane 1’100 wasu kuma 600,000 suka bar muhallansu a kasar ta Kenya.
An dai gudanar zaben cikin kwanciyar hankali a yawancin wurare inda aka ci gaba da zaben a wasu rumfunan har bayan lokacin rufe jefa kuri’a wato karfe 5:00 na yamma agogon kasar.
Kafin dai wani dan takara ya lashe zaben shugaban kasar yana kukatar ya samu sama da kashi 50% na yawan kuri’un da kuma kashi 25% na yawan kuri’un da aka jefa a larduna 24 daga cikin 47 da kasar ta Kenya ke da su.
Idan ba wanda ya samu wannan to za a je zageye na biyu na zaben tsakanin ‘yan takara biyu da ke kan gaba.
Duk da cewa an riga an samu sakamakon wasu mazabun, akwai yiwuwar a yi dakon kwana da kwanaki kafin cikakken sakamakon zaben ya fito.
Shi dai shugaba Uhuru Kenyatta dake kan mulki ya yi alkawarin mutunta zabin da jama’a suka yi.
Baya ga zaben shugaban kasar akwai kuma takara mai zafi a zabukan ‘yan majalisar dokoki da kuma na shugabannin kananan hukumomi.
Fatan al’umar Kenya shi ne a gudanar da sahihin zabe, karbabbe, wanda zai tabatar da dorewar kasar ta fuskar siyasa da kuma tattalin arzikinta, a yanayin da ake ciki mai matukar muhimmanci.