✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen Jibiya sun fara sare bishiyoyin kan hanya saboda matsalar tsaro

Sun ce za su sare bishiyoyin dukkan hanyoyin shiga garin

A wani mataki na kare kansu daga kalubalen tsaro, mutanen Karamar Hukumar Jibiya da ke Jihar Katsina sun fara sare bishiyoyin manyan hanyoyin shiga garin.

Sun ce sun dauki matakin ne domin samar da sarari ganin cewa ’yan bindigar daji na amfani da duhun bishiyoyin wajen tare motoci suna shiga daji da su.

Alhaji Surajo Agaji, daya daga cikin ’yan kungiyar da ke aiwatar da aikin ya shaida wa Aminiya cewa, sun dauki matakin ne domin bayar da ta su gudunmuwar ta fuska tsaron yankin.

Ya kuma sha alwashin cewa aikin ba zai tsaya a iya hanyar Jibiya zuwa Katsina ba, dukkan hanyoyin shiga garin muddin suna da duhun itatuwan bakin hanya sai sun sare su.

“A yanzu mun kashe sama da naira dubu 200 don gudanar da wannan aiki. Acikin kudin ne muka biya kudin hayar injin mai yankan itace, sayen ruwa da dan abincin da masu aikin za su ci, biyan motar da ke tafiya da mu da sauransu.

“Yanzu haka, daga cikin wadannan kudade ina jin bai wuce Naira 5,000 ba a hannu sannan ga aikin yanzu ma aka fara yin shi.

“Bisa wannan ne muke neman gudunmuwar al’umma don ganin mun kammala wannan aiki wanda tuni aka fara ganin fa’idar shi,” in ji Alhaji Surajo.