✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen Daura sun shirya wa Buhari gagarumar tarba ranar da zai bar mulki

Za a gudanar da hawa na musamman da wasannin kokawa da shadi saboda murnar tarbar shi

Garin Daura, mahaifar Shugaban Kasa mai barin gado, Muhammadu Buhari, ya dauki harami kamar na jajiberin Sallah a shirye-shiryen bikin karbar shi bayan kammala wa’adin mulkinsa ranar Litinin mai zuwa.

Sarkin Daura, Umar Farouq Umar ne dai ke jagorantar jerin shirye-shiryen a masarautar da ke Jihar Katsina.

A ranar Litinin, 29 ga watan Mayu mai zuwa ce dai ake sa ran Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa na shekara takwas, inda zai mika ragamar ga magajinsa, Bola Ahmed Tinubu.

Lokacin da wakilinmu ya ziyarci garin ranar Asabar, ya iske Sarkin a shigar da ba a saba ganin shi a irin ta ba, yana duba shirye-shiryen da ake ta yi, domin tabbatar da cewa komai ya tafi kamar yadda aka tsara.

“Idan ba ka san Sarkin ba ko motar da yake hawa, ba ma zaka gane cewa shi ne yake zagayawa yana duba ayyukan ba. Wannan zai kara nuna maka irin muhimmancin da mai martaba Sarki ya ba wannan bikin tarbar,” in ji wata majiya da ke da kusanci da masarautar.

An shirya taron daba da kokawa da shadi

Domin karbar Buharin, [wanda suke kira da Bayajidda na biyu] a ranar Litinin mai zuwa, masarautar Daura ta shirya wani kasaitaccen bikin hawan dawakai (daba) na musamman.

Bugu da kari, Aminiya ta gano za a gudanar da wasan kokawa da shadi/sharo na Fulani.

Sarkin na Daura ne dai ya fara bayyana labarin shirya hawan lokacin da Gwamnan Jihar, Aminu Bello Masari ya kai masa ziyarar bankwana a makon da ya gabata.

“Ina son na sanar da mai girma Gwamna cewa muna shirya wata kasaitacciyar daba domin tarbar danmu kuma shugabanmu, Muhammadu Buhari, kuma Bayajidda na biyu. Saboda haka, muna gayyatarka da ka zo domin kai ma ka hau doki, ko dai a matsayinka mai rike da sarautar Matawallen Hausa a masarautar, ko kuma a matsayin babban bako,” in ji Sarkin na Daura.

Gidan Buhari na Daura ya sha kwaskwarima

A bisa al’ada dai, duk Shugaban Kasar da zai bar mulki, a kan ba shi dama ya fadi duk inda yake so Najeriya a gina masa gidan da zai zauna bayan ya bar mulki.

To sai dai shi Buhari, tsohon gidansa na Daura ne kawai ya zabi a yi wa fenti, ba tare da an sake wani gini a ciki ba, ballantana a gina masa sabo.

Ko kafin ya zama Shugaban Kasa a shekara ta 2015, Buhari dai na sintiri ne tsakanin gidajensa na Daura da na Kaduna, wanda aka yi ittifakin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Shehu Musa ’Yar’aduwa ne ya ba shi.

To sai dai har ila yau, Amniya ta gano cewa shi ma gidan na Kaduna, wanda yake kan titin Sultan Road, yanzu haka yana can ana yi masa makamanciyar irin waccan kwaskwarimar.