Bayan dakatar da mukaddashin shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), rahotanni na cewa Fadar Shugaban Kasa ta fara neman wanda zai maye gurbin Ibrahim Magu a kujerar.
Daga cikin mutanen da ake hasashen za su maye gurbin nasa akwai wasu tsoffin mataimakan sufeta janar na ‘yan sanda biyu da wasu kwamishinonin ‘yan sanda masu ci guda biyu.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wani kwamiti karkashin jagorancin tsohon Mai Shari’a Ayo Salami ke bincikar Magu a kan zarge-zargen badakala.
Su wa ake hasashe za su maye gurbinsa
Tun bayan dakatar da Magu wasu rahotanni ke cewa tuni fadar shugaban kasa ta fara neman wanda zai maye gaje shi a kujerar.
- ‘Binciken Magu ya nuna ba wanda ya fi karfin doka’
- Binciken Magu: Shin shugaban EFCC zai kai bantensa?
Wasu majiyoyi sun tabbatar cewa kwamitin ne ya bayar da shawarar dakatar da Magu don ya samu damar yin cikakken bincike a kan zargin.
Magu na fuskantar zarge-zarge daga Ministan Shari’a Abubakar Malami masu nasaba da karkatar da kadarorin da EFCC ta kwato daga hannun barayin gwamnati.
Rahotannin sun ce a watan Yuni Malami ya ba da sunayen wasu mutane uku da za a iya nadawa bayan ya ba da shawarar sallamar Magu daga shugabancin hukumar.
Daga cikin sunayen akwai mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda, Mohammed Sani Usman mai ritaya, kwamishinan ‘yan sanda na Babban Birnin Tarayya Abuja, Bala Ciroma da kuma wani mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda daga jihar Kebbi.
Wata majiyar kuma ta ce akwai yiwuwar a kara da kwamishinan ‘yan sanda na jihar Enugu, Ahmad Abdurrahman da kuma mataimakin kwamishinan ‘yan sanda DCP Mohammed Abba Umar.
Abba, wanda dan asalin jihar Kano ne na daga cikin manyan jami’an hukumar EFCC kuma yanzu shi ne ke rike da mukamin daraktan ayyuka a hukumar.
Wata majiyar kuma na cewa mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda, DIG Sani Muhammad Gwallaga na iya maye gurbin Magun.