Adadin mutanen da suka mutu a hatsarin jirgin saman sojin kasar Philippines ya kai 52, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar ranar Litinin.
Rahotanni dai sun ce jirgin na sojoji kirar C-130 ya fadi ne a garin Patikulda ke Tsibirin Jolo a Kudancin kasar ranar Lahadi, kuma tuni masu bincike suka dukufa wajen gano musabbabinsa.
Biyu daga cikin sojojin da suka jikkata sakamakon hatsarin dai daga bisani sun mutu a asibiti, lamarin da ya kawo adadin sojojin da suka mutu zuwa 49.
Garin na Patikul dai na da nisan kilomita 1,000 daga babban birnin kasar na Manila, kamar yadda Sakataren Tsaron kasar, Delfin Lorenzana ya tabbatar.
Sai dai ya ce adadin fararen hular da suka mutu ya zuwa yanzu mutum uku ne, yayin da wasu sojoji 47 da fararen hula hudu da suka jikkata na can suna samun kulawa a asibiti.
Wani ganau a inda hatsarin ya faru ya ce wasu daga cikin wadanda suka tsira sun rika dirowa daga jirgin gabanin fadowarsa a kasa.
Jirgin dai ya fado kasa ne sannan ya kama da wuta.
Hotuna sun nuna yadda wasu daga cikin fuka-fukan jirgin basu fita daga jikinsa ba, yayin da wasu kuma suka balle suka kama ci da wuta a jikin bishiyoyin kwakwa.
Tuni dai sojoji suka yi wa wajen kawanya domin neman akwatin bayanan jirgin domin taimakawa a binciken da suke yi.
Jirgin dai na dauke da sojoji 96, ciki har da matuka uku da kuma sauran ma’aikatan jirgi biyar a ciki.
Yawancin sojojin da ke cikin jirgin dai sabbin yayewa ne da aka tura zuwa yankin na Jolo domin yaki da ’yan ta’adda na Abu-Sayyaf a kasar. (NAN)