✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutanen da girgizar kasa ta kashe a Turkiya da Syria sun zarta dubu 36

Duk da debe tsammani, an ceto wasu mutane hudu a jiya Lahadi da ransu.

Adadin mamatan da aka samu sakamakon girgizar kasar da ta auku a Turkiyya da Syria sun zarta dubu 36.

Wannan na zuwa ne a yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta koka a kan yadda ta gaza kai kayayyakin agajin da ake matukar bukata a yankunan Syria da yaki ya daidaita kuma aka samu girgizar kasar.

MDD ta yi kashedin cewa adadin mutanen da suka mutu a ibtila’in girgizar kasar da ta afka wa Turkiya da Syria ya iya zarce mutum dubu 37.

Duk da cewa wani ayari da ya biyo ta Turkiya ya isa Arewa maso Yammacin Syria da kayayyakin agajin, amma Shugaban Hukumar Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya, Martin Griffiths ya ce akwai abubuwa da dama da ake bukata don taimaka wa miliyoyin mutanen da suka rasa muhallansu a Syria.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Griffiths ya ce al’ummar Arewa maso Yammacin Syria na matukar neman agaji daga kasashen duniya, amma kuma bai isa gare su ba, saboda haka dole su rika jin an yi watsi da su.

Ya zuwa yanzu adadin wadanda suka mutu sakamakon wannan girgizar kasa ya haura dubu 36 a wannan Litinin, kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ce yana iya ninkawa.

A yayin da masu aikion ceto ke debe tsammani kan ragowar masu sauran numfashi a baraguzan gine-gine a Turkiyya da Siriya, adadin wadanda suka rasu na dada karuwa.

Turkiyya ta ce za ta kai karar wasu kamfanonin gine-ginen kasar da ta zarga da sakaci wajen kara ta’azzara mummunar girgizar kasar da ta yi mummunan illa.

Mataimakin Shugaban Turkiyya, Fuat Oktay, ya bayyana cewa akwai akalla kamfanoni 130 da ke shirin shiga komar mahukunta kan zarginsu da rashin samar da gine-gine mafi inganci a wurare da dama.

Duk da debe tsammanin da ake na samun ragowar masu sauran numfashi, an ceto wasu mutane hudu a jiya Lahadi da ransu.

Hukumomi da ma’aikatan lafiya sun ce an yi asarar rayuka 31,643 a Turkiya, kana mutane 4,614 suka mutu a Syria, biyo bayan girgizar kasa mai karfin kusan maki 8 da ta auku a Litinin da ta wuce, lamarin da ya kai jimillar mamata dubu 36 da 257.