✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutanen da COVID-19 ta kashe a Gombe sun kai 60

Kimanin mutane 60 ne suka mutu a sanadiyar cutar COVID-19,  yayin da 2,776 suka mutu 2,690 suka warke a Jihar Gombe cikin shekara daya, inji…

Kimanin mutane 60 ne suka mutu a sanadiyar cutar COVID-19,  yayin da 2,776 suka mutu 2,690 suka warke a Jihar Gombe cikin shekara daya, inji Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dokta Habu Dahiru.

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Gombe, lokacin da yake zantawa da manema labarai kan matakan kariya na bullar sabuwar cutar Omicron.

Dokta Dahiru, ya ce an samu karuwar bullar cutar da kimanin kaso 124.4 cikin 100 a Jihar, sannan jama’a ba sa daukar matakan kariya yadda ya kamata.

Ya ja hankalin duk wanda suka karbi rigakafin karo na farko da na biyu da su daure su karbi kashi na uku don samun cikakkiyar kariya daga kwayar cutar.

A cewar Kwamishinan, yanzu haka Jihar na shirin karbar kwalaben kariya rigakafin cutar kimanin 109,000 na kamfanin Pfizer.

Dokta Habu ya kuma yi kira ga jama’a da cewa ganin za a shiga bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara, mutane su dauki matakan kariya kamar sanya takunkumi da wanke hannu da ba da tazara, musamman a lokacin da suka shiga cikin jama’a.

Daga nan sai ya sake jan hankalin jama’ar Jihar cewa duk da samfurin cutar na Omicron ba ya kisa kamar ta Kwarona, ya zama wajibi a kiyaye daukar matakan kariya.