Mazauna garin Marte a Jihar Borno na gudun tsira da rayukansu a yayin da dakarun gwamnati ke gwabza fada da mayakan Boko Haram.
Daruruwan fararen hula ne suka bar garin bayan mayakan dandazon Boko Haram sun kai hari a kan wani sansanin soji inda suka kona gine-gine a daura a Tabkin Chadi.
- Abubuwan da ya kamata ku sani game da yakin basasar Najeriya
- Kannywood ta zama kasuwar bukata – Zango
- Bom ya kashe sojoji 5, ya jikkata 15 a Borno
- Iyaye sun yi karar saurayin ’yarsu kan fasa auren ta
“Abin takaici ne labarin da muka samu ce da misalin karfe takwas na dare sojoji sun shafe awanni suna gwabza yaki da ’yan Boko Haram.
“Yanzu da muke magana, daruruwan mutanen da suka koma gidajensu sun tsere suna gudun hiji a Dikwa.
“Sojojin sun yi kokari amma labarin da muke samju shi ne daruruwan mayakan kungiyar ne suka kai harin, saboda haka sojojinmu na bukatar addu’a,” inji majiyarmu.
Wani jami’in Gwamnatin Jihar Borno ya shaida wa Aminiya cewa daruruwan fararen hula sun kwana ne a cikin dazuwa, wasunsu kuma sun taka zuwa garin Dikwa mai nisan kilomita 25 daga Marte, domin samun tsira.
Mayakan Boko Haram sun kai wa garin Marte harin na ranar Juma’a ne bayan mazauna sun koma gidajensu daga gudun hijira, lamarin da ya sake tilasta msusu tserewa zuwa cikin dazuka.
Majiyarmu ta tsaro ta ce mayakan sun kai wa sansanin sojin hari ne domi su jefa tsoro a zukatan mazauan kauyen.
Sai dai ya ce zuwa safiyar Asabar an tura karin sojoji daga Dikwa domin ragarzagar ’yan ta’addar, sai dai babu cikakken bayani kan halin da ake ciki, zuwa lokacin kammala hada wannan rahoto.
A ranar 1 ga watan Disamban 2020 ne Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Umaru Khadafur ya mayar da iyalai 500 da suka kunshi mutum 2,870 garin na Marte bayan sun yi kusan shekara shida suna gudun hijira a Jamhuriyar Nijar.